Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, September 24, 2017

TAURARINMU..... MARIGAYI INJINIYA IBRAHIM BAYI.

HADEJIA A YAU!


Jama'a barkanmu da wannan lokaci, da fatan kuna lafiya. Ga kadan daga Tarihin Rayuwar Marigayi Injiniya Ibrahim Bayi, wadda shima yana cikin Sahun mutanen da muka kirasu da suna........ "TAURARINMU"

An haifi Engineer Ibrahim Bayi a garin Hadejia Mahaifinsa shine Mallam Muhammadu Sarkin Yarin Hadejia, ya fara karatu a Makarantar Elementary ta Hadejia Wadda ake kira Abdulkadir Primary a yanzu a shekarar 1939 zuwa 1942. Sannan ya tafi makarantar Middle dake kano a shekarar 1942 zuwa 1945. Daga nan Ibrahim Bayi ya tafi makarantar Barewa College a shekara ta 1945 inda ya gama a shekarar 1948. Bayan ya dawo Hadejia ya tabawa N. A. Aiki na 'yan shekaru a ofishin Wakilin Sana'a sai ya koma Kaduna inda anan ne ya samu damar zuwa makarantar Brighton College of Technology wadda yanzu ake kiranta University of Sussex ta Brighton a shekarar 1958 zuwa 1962, Inda ya samu shaidar takardar Diploma in mechanical engineering.

Engineer Ibrahim Bayi yayi Ayyuka a wurare daban daban a fadin Nigeria, kuma ya zama Bubban Engineer a shekarar 1966. An zabe shi member na cibiyar Harkokin Masana'antu ta Birtaniya (MI MECH E.) Yayi aiki a Kamfanin Harkokin tsaro a shekarar 1968, inda ya zama Janar Manaja a Shekarar 1972. A shekarar 1976 zuwa 1980 ya zama shugaban hukumar bada ruwan sha ta jihar Kano (WRECA). Wannan Bawan Allah ya samarwa mutane Ayyuka daban daban, sannan ta dalilinsa Hadejia ta samu ma'aikatun Gwamnatin Tarayya kamar su Nepa, Nitel, Post Office da sauransu. 

Engineer Ibrahim Bayi ya samu lambar girma ta hannun gwamnatin Koriya ta Kudu a shekarar 1982, yayi ritaya daga aiki a shekarar 1985. Sannan ya zama shugaban kwamatin gudanarwa a kwalejin kimiyya da fasaha dake Mubi tsakanin 1986 zuwa 1993. Ya zama member a hukumar Jigawa resources Development Agency 1995 zuwa 1999.  Engineer Ibrahim Bayi ya rasu a gidansa dake Kaduna Ranar Laraba 9/July/2014, ya rasu yana da shekara 84 a Duniya. Ya bar matar Aure da 'ya'ya goma (10) da Jikoki Ashirin da biyar (25). Allah ya gafarta masa da rahma tare da Iyayen mu.

Sunday, August 6, 2017

AN RATAYAWA SARKIN KANO SUNUSI LAMBAR GIRMA TA K.B.E.

HADEJIA A YAU!

AN RATAYA WA SARKIN KANO SUNUSI LAMBAR GIRMA TA K.B.E.

A cikin watan Satumba/1958, bubban Razdan na Kano Sir. Gawain Bell ya ratayawa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi lambar Girma ta K.B.E. anyi gagarumin Hwan Daba inda aka kewaya gari daga nan aka nufo Ƙofar Fada inda anan ne aka ratayawa Sarki wannan lamba. Mutanen da sukayi kallon Dabar sun kwatanta ta da Dabar da aka yiwa Sarauniya. Sarakunan Ƙasar nan da yawa da manyan Ma'aikatan Gwamnati ne suka halarci wannan taro, a cikinsu harda Firimiyan Jihar Arewa Sir. Ahmadu Bello da Ministocinsa, har ma da Mukaddashin firayim Minista Sir. Abubakar Tafawa Ɓalewa.

Kimanin mutane Dubu Talatin (30,000) ne suka halarci taron shagalin Baiwa Sarki Sunusi wannan lambar Girma, ciki da wajen Jihar Arewa, abin sha'awa Sarkin Musulmi Sir. Abubakar da ya halarci taron ance rabonsa da Kano shekara 16 kenan. Firayim Minista bai samu zuwa ba amma Muhammadu Ribadu ya wakilce shi. Cikin manyan Baƙi harda Chif Jojin Sudan wadda Gwamnatin Arewa ta gayyato domin binciken Al'amuran Shari'ah a wannan Jiha, da kuma Wakilin Amurka a Nijeriya. Bayan an kimtsa duk manyan Baƙi sun zauna a Cikin Ƙwatattun Rumfuna sai Gwamnan Arewa ya nufo Ƙofar Mata inda aka je aka taryoshi akan Dawaki, Sarkin Kano da Hakimai da mahaya Dawaki duk aka tafi taryen Gwamna. Bayan sun gaisa da Sarki shima Gwamna sai ya hau Doki aka nufi ƙofar Kudu inda ake Shagalin bikin, ‘yan Doka masu Badujala ne suka share musu hanya suna tafe suna kiɗa da busa, Gwamna na tafe tare da Muƙaddashin Razdan na Kano Mr. melinctock. Sarki kuma na biye dasu da Dogarai da ‘yan Sulke da ‘yan Kwalkwali har zuwa ƙofar Kudu. 

Sarkin Musulmi Abubakar tare da Sarkin Gwandu sune suka kai Sarki Sunusi Rumfar da za’a rataya masa Lambar Girman, daga nan sai Razdan ya miƙe ya karanta saƙon Sarauniya na bayar da Lambar, sannan sai Gwamna ya miƙe ya Ratayawa Sarkin Kano Sunusi lambar, sai wuri ya kaure da Tafi da shewa da kiɗe kiɗe da Bushe bushe don murna.


WANNAN DARAJA TA KOWA CE.
Sarkin Kano Sunusi ya miƙe yayi jawabi inda ya fara da godewa Allah (swa), sannan yace “Ina godiya ga Allah wadda da ikonsa ne wannan abu ya kasance a rana irin ta yau, sannan ina ƙara godiya ga Mai Martaba Sarauniya saboda wannan Daraja da ta bani, tare da shaidar Amincewa a rataya min a gaban Jama’a. Wannan Daraja ta shafi kowa ba ƙasar Kano kawai ba, harda duk Jihar Arewa. Na tabbatar da wannan shine lokaci na biyu da aka bada irin wannan Lambar girma a Jihar Arewa, mu duka munyi farin ciki da Alfahari a lokacin da Sarkin Ingila King George na 6 ya baiwa Sarkin Musulmi irin wannan lambar, to ina Alfahari da cewa nine na Biyu da aka baiwa wannan lamba, nayi Alƙawari zanyi matuƙar ƙoƙarin da zan iya in nuna na dace da wannan lamba da aka bani.
ZAMA MASU ZUMUNCI DA INGILA.
Da Sarkin Kano Sir. Muhammadu Sunusi ya Juyo wajen Maganar Samun Mulkin Kai sai yace, "Yau saura watanni goma sha takwas 18, muke zaton samun cikakken mulkin kai na Nijeriya. Mun lura da irin wahalce wahalcen dake gabanmu, amma duk lokacin da na hangi waɗannan wahalce wahalce nakan ji daɗi idan na tuna ƙasar nan zata zama ɗaya daga cikin ƙasashen da suke haɗa kai da Ingila. Da taimakonsu da kuma Jagoransa, in Allah ya yarda ƙasarmu zatayi ta ci gaba da Arziƙi."

Bayan Sarkin Kano Sunusi ya gama Jawabi sai aka Sallami kowa, duka manyan Baƙi suka tafi masauƙi. Da daddare kuwa Jam'iyyar NPC ta shirya wata ƙasaitacciyar rawa a Randabu Hotel saboda murnar bayar da lamba girma ga Sarkin Kano Muhammadu Sunusi. Alhaji Mai-wada M.H.A. shine ya shugabanci bikin Rawar.

MADOGARA...
Gaskiya Ta fi Kobo
EAP/485-11-397