content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!: Jan 15, 2013

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, January 15, 2013

TARIHIN RAYUWAR SIR. AHMADU BELLO (SARDAUNA) 15/01/2013.

Easily Upload Your Images To Myspace
An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya. Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wadda yana daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.


Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina. Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi. Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Sir Ahmadu Bello ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966. Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun 'yancin kai..

Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista. Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.


An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.