content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!: 12/01/2014 - 01/01/2015

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Saturday, December 20, 2014

ZIYARA DA AMFANINTA.

a.

r">
Ziyara wani Nau'i ne na zumunci wanda mutane suke aiwatar da ita domin sada zumunci ga 'yan'uwa da abokan Arziki. zumunci wata irin halayya ce ta kwarai wacce ke sadar da dangantaka ta nasaba tsakanin ’yan'uwa ko bare. Zumunci ne ke kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali da fahimtar juna tsakanin al’umma.

Ta hanyoyin da mutum zai bi ya inganta zumunci shine, kaiwa ziyara ga 'yan'uwansa kamar kaka, uba kokuma kanin mahaifi ko kanin mahaifiya da sauransu. Ta haka ne mutum zai gane irin yadda Alaqarsa take da 'yan uwansa na nesa ko na kusa. Haka kuma kowa yana da iya kimar zumuncin da zai gudanar a tsakaninsa da wani. Kamar yadda Hausawa suka ce zumunta a kafa take, to wannan gaskiya ne,domin
kuwa daya daga cikin manyan ginshikan zumunta shi ne ziyartar juna. Idan ka kula da zumunci shike sa mutum ya niki gari zuwa gidan abokinka ko wani dan'uwanka, ko bare musamman domin ganin yadda yake. Wannan ziyara kawai, ita ke haddasa kauna da mutunci mai dorewa a tsakanin al’umma.

A shekarun baya kamar shekara kamar goma zuwa sama,saboda muhimmancin ranar Juma'a,iyaye sukan je da 'ya'yansu gidajen 'yan'uwansu da Abokan Arziki domin gaisawa wanda hakan yana nuna ana nusar da yara ne da kaiwa ziyara ga 'yan uwansu. Harma yara suke kiran wannan ziyara da yawon Juma'a. Amma saboda shagaltar da zuciya irin ta shaidan tasa wannan kyakkyawan Aiki na ziyara ya fara ja baya ga yara harma da manyan a wannan zamani,domin shi bubba yana tunanin ai in yaje zai bada kudi, sannan yaro yana tunanin kar yaje ba'a bashi kudi ba.

Wednesday, December 3, 2014

TAKAITACCEN TARIHIN HASHIM UBALE YUSUF..

Hadejia A yau!

An haifi Hashim Ubale Yusufu a Garun Gabas da ke cikin yankin Karamar Hukumar Mallam Madori ta yanzu, A ranar 21 ga Satumba na shekarar 1956. Ya fara karatunsa a makarantar firamare a nan Garun Gabas inda ya fita da kyakkyawan sakamako a matsayin dalibi mafi kwazo da hazaka Daga nan ya wuce zuwa Sakandaren gwamnati dake Birnin Kudu inda ya yi karatu daga 1969 zuwa 1973, lokacin da ya rubuta jarrawar makarantun sakandare ta Afirka ta Yamma wato WASC.

Ya halarci Makarantar Koyon ilimi mai zurfi ta Kano, wato College of Advanced Studies daga 1973 zuwa 1975, inda ya fita da babbar takardar shaida, wato Higher School Certificate. Daga nan kuma ya sami shiga jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria inda ya yi karatun digiri a fannin ilimin harhada magunguna (wato pharmacy) wanda ya gama a shekarar 1981.Bayan ya kammala karatun jami-a, sai sai ya tafi aikin bautar kasa a jihar Imo inda aka tura shi Federal Polytechnic da ke garin Afikpo -Okposi inda ya yi aiki a matsayin mai bayar da magani na wannan makarantar da kuma koyar da darasin chemistry daga 1982 zuwa 1983.Hashim ya fara aiki tun daga matakin karamin ma'aikaci inda a tsawon shekaru ya taka matakai daban daban har zuwa matsayin darakta a hukumar kula da tsaftar abinci da magunguna a Nigeria, da kuma bubban sakatare wato permanent secretary.

Ya fara aiki a shekarar 1974 a matsayinsa na Mataimakin Jami'in gandun daji a karkashin sashen kula da gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa bubban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda yayi aiki amatsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi a cikin shekarar 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka daukeshi aiki a karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya. Daga 1985 zuwa 1987, ya yi aiki a cibiyar sayar da magani ta Lafiya Pharmacy dake garin Hadejia, wadda ta kasance daya daga cikin cibiyoyin sayar da magani da aka bude a wancan lokacin. Bayan daukar lokaci yana aiki karkashin gwamnati,sai ya tsallaka zuwa ma'aikatu masu zaman kansu inda ya yi aiki a kamfanonin sayar da magunguna na NAMCO da kuma ANHEL das u ke cikin binin Kano daga 1987 zuwa 1989. Haka nan ya yi aiki a da hukumar bada tallafin cigaba ta kasar Amurka wato USAID a matsayin jami’in gudanar da ayyuka na kasa karkashin shirin Inganta Lafiyar Iyali (wato Family Health Services).

A shekarar 1989, ya rike mukamin Mai bada shawara a gandun daji na tsohuwar Jihar Kano, sannan daga bisani ya canja aiki zuwa Babban Asibiti na Kano (wanda aka fi sani da asibitin Murtala a yanzu) inda ya yi aiki a matsayin jami'i mai bada magani na wucin-gadi tsakanin 1981 da 1982, inda kuma a shekarar 1983 aka dauke shi aiki karkashin Sashen Kula da ayyukan lafiya kuma aka tura shi Asibitin Murtala da ke Kano a matsayin Jami'in bayar da magani mai daraja ta daya.