content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, December 14, 2012

ALHAJI TIJJANI DODO HADEJIA.

Image Hosted by ImageTitan.com 
Hadejia a yau!
A ci gaba da kawo muku tarihin wadanda suka bada Gudun mawa a Kasar Hadejia, yau Aji kima ya kawo mana Kadan daga Irin Gudunmawar da Alh. Tijjani Dodo yake bayarwa!

Dattijo Alhaji Tijjani Dodo Hadejia Dan Baiwa ne, Wanda ba kowa ya san hakan ba.Wannan mutumin baya kasa a gwiwa ganin al'uma sun ci gaba. Wannan yasa ya wajabtarwa kansa fafatawa a harkokin rayuwa daban-daban domin samarwa al'uma mafita. Duk wurin da ka leka zaka hango shi saboda Jajircewa da gina rayuwar sa da yayi akan Gwagwarmaya. 

1.Dan kasuwa ne,

2.Dan siyasa ne,

3.Ba sarake ne,

4.Dan kungiyar aikin gayya ne,

5.Dan kungiyar Achaba ne,

6.Dan kungiyar matasa ne,

7.Dan kungiyar yan kasuwa ne,

8.Dan kungiyar ma'aikatan gwamnanti ne

9.Dan kungiyar kwallon kasa ne,

10.Dan kwamatin hawan sallah ne,

11.Dan kwamatin gyaran makabirta ne.

12.Dan kwamatin jinga ne,

13.Dan kwatin gayaran masallaci

14.Dan kwamatin gyaran gari.

15.Dan kungiyar raya al'adun Gargajiya.


Yanzu haka shi ne shugaban aikin gayya na Hadejia,
shi ne kuma shugaban yan Achaba, haka kuma dogari ne a fadar Hadejia. Lalle Juyi Goma sai Wake Inji masu Iya magana.

A hannu daya kuma dan siyasa,dan kasuwa, Jama'a ya kamata mu jinjinawa wannan bawan Allah, Allah ya bamu dubu masu amfani irinsa.

Wannan hotonsa ne yana bada hannu. Bai yadda yaga abu bai yi iya bakin kokarinsa ba. Idan na magana ne zaiyi idan da karfinsa ne zaiyi idan da aljihunsa ne sai yayi.

Allah ya saka da alherinsa.

Monday, December 10, 2012

TARIHIN SHEIKH JA'AFAR MAHMOOD ADAM.

Easily Upload Your Images To Myspace
Free Music MARIGAYI SHEIKH JA'AFAR MAHMUD ADAM. GIDANSU, HAIFUWARSA DA .TASHINSA. Babban Shehin Malami, Kwararren mai Tafsiri, Gawurtaccen mai Da’awah,Baban Salim Ja’afar dan Mahmoodu dan Adamu, An haifeshi a yankin Daura a jihar Katsina a Shekara ta 1961. Gidansu Malam Ja’afar, Gidane da su ke kulawa da Ilimin Addini da Haddar Alqu’ani, Kakansa ya kasance yana karantar da Littattafan Fiqhu da Yaren Larabci, Wasu cikin ‘Ya’yansa kuma har sun haddace Alqur’ani. Malamin farko da ya fara dorawa Malam Ja’afar karatun Alqur’ani, Wani Malami ne mazaunin gari Daura mai suna Malam Magaji, yana masa matsayin Babban Yaya ne, domin sun hada dangantaka da shi a Kakanninsu, Shine farkon wanda ya fara koya masa Bakaken Larabci, Wannan Malami, Mahaddacin Alqur’ani ne tun a wancan Lokaci. Baban Salim ya fara koyon karatun Alqur’ani ne a hannun Mijin Babbar Yayarsa mai suna Malam Haruna, wanda shima yana masa matsayin Dan’uwa ne, Daga hannun wannan Malamin ne aka maida Malam Ja’afar hannun wani Malamin kuma Dan’uwansa a kauyen Kuza mai suna Baba Rabe, Wannan Malamin shine ya kaurato tare da Baban Salim zuwa garin Kano a shekarar 1971 ko 1972, Sun sauka a gidan wani Gawurtaccen Mahaddacin Alqur’ani dan kasar Nijer ne mai suna Malam Abdullahi dan Zarmu a unguwar Fage a cikin birnin Kano. Baba Rabe yayi fatar ganin Malam Ja’afar ya haddace Alqur'ani tun yana raye, Amma Allah bai so hakan ya faru a Idanunsa ba, Wannan Malamin ya rasu a shekarar 1977 ne, Shi kuma Malam Ja’afar ya haddace Alqur’ani ne a shekarar 1978 DAGA KARATUN ALLO ZUWA JAMI’A Baban Salim ya haddace Littafin Allah mai girma bai wuce da shekara sha Bakwai ba. Ya fara karatun Alqur’ani gadan-gadan ne a hannun Malam Abdullahi Mutumin Nijar, Malami ne da aka san shi da tsanantawa Almajiransa da matsa musu kan inganta haddar Alqur’ani, Ina ganin wannan matsawar ta shafi har Baban Salim, Domin sakamakonta shine wannan ingantacciyar haddar Alqur’ani da Allah ya baiwa Baban Salim, wacce ba kasafai a ke samun Mahaddata Alqu’ani da irinta ba, In ban da ‘yan kadan cikin Tsarakunsa. Malam bai haddace Alqur’ani a hanun Malam Rabe dan Zarmu ba kamar yadda Malamin yayi fata, Dalili kuwa shine Malam Ja’afar da Tsarakunsa a wancan lokaci, wasan kwallon kafa da zuwa kallonta ya dauke musu hankali kan tsayuwar daka kan haddar Alqur’ani, Wannan ya sa, Malam Rabe ya daukeshi daga hanun Malam Dan Zarma ya maida shi garin Hadejiya ya damka shi a hannun wani Malami dan asalin gari Daura amma Mazaunin Hadejiya mai suna Malam Safiyanu,wanda shima Dan’uwa ne ga Malam Ja’afar domin sun hada dangi da shi ta Kakanninsu. Malam Rabe yayi masa haka ne don ya raba shi da kayaniyar Birni da kuma damuwa da Lamarin kwallon Kafa, Maiyiwuwa hakan zai sa shi ya maida hankali kan haddar Alqur’ani, Lalle kuwa hakan ya faru, domin Baban Salin a can ya kamala haddar Alqur’ani bayan rasuwar Malam Rabe. Bayan fara baiyyanar Kungiyoyin Musulunci a Nigeria, Musamman ma Kungiyar Izala, Sai jayayya ta yi yawa tsakanin Mutane kan wassu Mas’aloli kamar ; Hukuncin Salatul Fatih, matsayin Darikun Sufaye, Hukuncin Durkuso a gaisuwa, Sadakar Fida’u bayan Mutuwa, Taron Suna da wassu Al’adun kasar Hausa, Wannan ya tilasta Malam Ja’afar neman Ilimin Littattafai. Malam Ja’afar ya shigar da kansa Makarantu Biyu lokaci guda. Ta farko a wata cibiya ta kasar Masar da ke garin Kano, Ta Biyu kuma wasu Azuzuwa ne da aka bude don yaki da Jahilci. Malam Ja’afar bai shiga Makarantar Firamare ba saboda a wannan lokaci sun yiwa wannan matakin karatun girma. Ya yi karatu a wadannan Makarantu na tsawon shekara Uku a jere daga 1980 zuwa 1983.