"" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Tuesday, January 15, 2013

TARIHIN RAYUWAR SIR. AHMADU BELLO (SARDAUNA) 15/01/2013.

Easily Upload Your Images To Myspace
An haifi Alhaji Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, a ranar 12 ga watan yuni na 1910 a garin Rabbar na jihar Sokoto dake Arewacin Najeriya. Kakansa shi ne sarkin Musulmi Bello, wadda yana daya daga cikin wadanda suka kafa daular Sokoto, kuma dane ga marigayi Mujaddadi Shehu Usman Dan Fodiyo.


Ahmadu Bello ya fara makaranta a garin Sokoto, sannan ya wuce zuwa makarantar horas da malamai ta Katsina. Kafin daga bisani Sultan ya nada shi malami a makarantar Middle School ta Sokoto.

A shekarar 1938 aka nada shi Sardaunan Sokoto bayan da ya gaza a yunkurin da yayi na zamowa Sultan, wato Sarkin Musulmi. Ya kuma halarci kasar Ingila domin yin karantu kan harkokin mulki a shekarar 1948.

Ya kuma fara shiga harkokin siyasa gadan-gadan bayan dawowarsa daga karatu, inda har aka zabe shi ya zamo mamba a majalisar dokoki ta Arewacin Najeriya. Ya kuma zama ministan ayyuka da raya kasa.

Sir Ahmadu Bello ya kasance Firimiyan farko na yankin Arewa daga shekarar 1954 zuwa 1966. Sannan ya jagoranci jam'iyyar NPC ta lashe kujeru da dama a zaben da aka gudanar bayan samun 'yancin kai..

Bayan kammala zabe, ya zabi ya ci gaba da kasancewa Firimiya, inda ya nada Abubakar Tafawa Balewa ya zamo Fira Minista. Ya taka rawa sosai wajen hada kan yankin Arewacin kasar wanda keda kabilu mabiya addini daban-daban, da kuma aiwatar da ayyuka na ci gaban kasa.


An kashe Ahmadu Bello a ranar 15 ga watan Janairun shekara ta 1966, bayan wani juyin mulki da wasu sojoji 'yan kabilar Ibo suka jagoranta.

Thursday, December 27, 2012

SAKON GODIYA DAGA MAI MARTABA SARKIN HADEJIA.

HADEJIA A YAU! Assalamu alaikum! Bayan gaisuwa irin ta Addinin musulunci tare da fatan Alkairi. Ina meka godiya da ban gajiya zuwa ga Mai girma Gwamnan Jihar Jigawa da Sanatoti da 'yan -Majalissu da Sarakunan Jihar Jigawa da sauran sarakunan Jihohi makwabta, Game da taya murna da akayi ta cika shekaru Goma a Kan Gadon Sarautar Hadejia! Kuma muna meka sakon godiya ga Jami'an tsaro da Mutanen Gari da Al'ummar Masarautar Hadejia sakamakon Hadin kai da suka bada aka gabatarda taro Lafiya. Allah ya saka da Alkairi. Hadejia A yau.
Kuma Muna meka sakon Godiya da ban gajiya ga Hakimai da Dagattai da Masu Unguwanni na wannan Masarauta mai Albarka. Allah ya saka da alkairi.

Muna kara godiya ga 'yan kwamitin wannan taro wadanda suka bada gudunmawa aka Gudanarda wannan taro Lafiya.

Kuma muna kara Addu'ah Allah ya kawo ci Gaba mai Amfani a Masarautar Hadejia! Allah ya tsaremu daga Masifu da fitintinu a kasarmu baki daya. Ameen. Hadejia A yau!