content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Thursday, May 14, 2015

YAN GUDUN HIJIRA...



YAN GUDUN HIJIRA!
Tun a lokacin da rikicin Boko Haram ya Addabi jihohin Borno da Yobe aka samu watsuwar 'yan gudun hijira a wasu sassa na Nigeria, ciki harda jihar Jigawa, kuma akasarin wadannan 'yan gudun hijira zakaga Mata ne da kankanan yara wadanda mafiya yawa suna a kasar Hadejia da kasar Gumel. A lokacin da suka fara zuwa wadannan yankuna saboda basu da abinda zasuyi dole wasu daga cikinsu suke bin masallatai da majlissai domin neman abinda zasuci abinci da yaransu. Abin tausayi zakaga yara da basu fi shekara 7 zuwa 10 ba suna bi kantuna da wurin zaman jama'a suna neman taimako, a kwanakin baya basuyi yawan da ya wuce kaga biyu ko uku ba a kullum amma yanzu abin sai karuwa yake wanda a kalla sai kaga goma zuwa sama a rana daya da mata da kananan yara abin tausayi. zaka gansu a kofar masallatai da kasuwa har da Bankuna wurin layin Atm. Dole mumini mai Imani ya tausayawa rayuwar wadannan bayin Allah domin ba a son ransu suka bar gidajensu da 'yan uwansu suka zo suke yin Bara ba! Saboda yawan kwararowarsu yasa jama'a sun fara kosawa ganin abin ya zama ba na kare ba, yanzu kullum a baka gansu a gidanka ba kaga biyar ko shida.

MASU HANNU DA SHUNI....

Hakika Masu hali sai sunyi amfani da damar da Allah ya basu wajen taimakon wadannnan bayin Allah da muhalli da Sutura da Abinci, da kuma kula da rayuwarsu musamman kananan yaran. yana da kyau masu hali su ware wani abu daga cikin Dukiyarsu don taimakon wadannan bayin Allah a matsayin Sadakatul-jariya.

GWAMNATI MAI JIRAN GADO...

Koda yake bani da masaniya game da yunkurin da Gwamnatin Jigawa tayi game da wadannan bayin Allah, kuma ban taba ganin wani wuri da aka ware don 'yan gudun hijira ba zanso in bada shawara ga Gwamnati mai jiran Gado, A karkashin mulkin ko jagorancin Jam'iyyar Apc, dasu fara duba wannan Matsalar ta 'yan Gudun Hijira kafin su fara Aiwatar da kowane Aiki domin ceto rayuwar wadannan Mata da kananan yara daga yin Bara, wanda hakan ya fara jefa wasu daga cikinsu zuwa ga halaka. An fara samun rade radin wadannan mata 'yan gudun hijira sun fara yin Arangama da wasu gurbatattun mutane suna yin lalata dasu suna basu kudi, har ma ance wasu da yawa sunyi cikin shege Allah ya kiyaye! Abin takaici sai kaga idan 'yan Hisbah suka kama mace tana lalata in suka bincika sai kaga 'yar gudun hijira ce. Kasan Dalilin da yasata cikin wannan hali?

SHAWARA GA GWAMNATI....

Ina bada shawara ga Gwamnati mai jiran gado da suyi la'akari da wannan matsalar domin su san ta yadda zasu bullowa wannan Al'amari, ya kamata Gwamnati ta samar musu mahalli na wucin gadi sannan ta sanya yaransu a Makaranta don ceto rayuwarsu. kuma Ina baiwa Gwamnati Shawara da ta sama musu sana'oi domin su dogara da kansu. misali Gwamnati zata iya amfani da makarantar koyon sana'a don koyawa Matan yanda ake yin SABULU, SAKA, DINKI,Da sauransu. Daga karshe ina Rokon Allah da kar ya nuna mana makamanciyar wannan Bala'i da zai sa mutum ya bar gidansa da iyalinsa ya tafi wani wuri yana yin abinda ko a Addini yana daga cikin Abu mai Kaskanci. Allah ka zaunar da kasarmu da Jiharmu lafiya.

Ismaila A Sabo Hadejia.
13/may/2015.

posted from Bloggeroid

Thursday, March 26, 2015

TAKOKO GARIN SARKI BUHARI...

TAKOKO GARIN SARKI BUHARI...



Garin Takoko yana daya daga cikin garuruwan Tarihi a Masarautar Hadejia, kuma yana Arewa da garin Mairakumi wanda take karkashin karamar hukumar Mallammadori, Takoko tana karkashin Mulkin Hakimin Garungabas. A lokacin da aka cire Sarkin Hadejia Buhari daga Sarauta ya koma garin Takoko da zama shi da Mutanensa inda kuma anan ne ya zauna tsawon lokaci yana kai hare hare ga kasar Gumel, Damagaram da wasu sassa na yankin Gorgaram (Bade). A zamansa na wannan gari ya samu goyon baya daga Daular Shehun Borno da kuma Machina, sakamakon karesu da yayi daga hare hare daga Mayakan Damagaram.

Bayan cireshi daga mulki da akayi ya koma Takoko Sarkin Hadejia Buhari ya zama Barazana ga Sarakunan Daular Usmaniyya, domin suna tunanin idan aka barshi a wannan gari to Daular Borno zatayi Amfani da karfin mayakansa ta rusa Daular Usmaniyya. Dan haka sai sukayi shawarar suje su yakeshi su kama shi kokuma su kashe shi, sai aka hada mayaka daga kano, katagum, Bauchi, Zamfara da sauransu.

YAKIN TAKOKO:-
Bayan an nada Ahmadu a matsayin Sarkin Hadejia, sauran Magoya bayan shi Buhari sai suma suka bar Hadejia suka koma Takoko inda Buhari yake suka zauna tare. Sarkin Hadejia Buhari anan ya zauna tsakanin Takoko da Shafowa a Arewacin Hadejia da mutanensa kuma yake tafiyar da wannan yankin. Kuma iyakar Hadejia ce da Damagaram da Machina ta Arewa maso Gabas wato yankin Niger da kuma Borno. Kuma Buhari ya bada Gudun mawa sosai a wannan Yankin wajen karesu daga barazanar mayaka, kuma a wannan zama da yayi a Takoko Buhari ya samu kyakkyawar dangantaka da Sarkin Machina da kuma Shehun Borno Umar wanda ya mulki Borno a wannan shekara (1835-1880) wannan dangantaka ta karawa Sarki Buhari kwarewa a yake yake.

(Bishiyar da Sarki Buhari yake hutawa, tana nan a gabas da garin Takoko).


A shekarar 1851, Sarkin Musulmi Alu Bubba yayi shirin ya dauki matakin Karshe akan Buhari, saboda yana tunanin Shehun Borno zai iya amfani da Buhari ya rusa Daular Sokoto saboda ya zame musu Barazana a Arewa Maso Gabas.
A wannan lokacin kuma Dan Galadiman Sokoto ya hada Mayaka daga Hadejia,Kano,Katagum,Misau da Jama'are zuwa Takoko.

A wannan lokacin kuma Buhari da mutanensa sun fita kudu da garin shafowa a lokacin Sarkin Machina ya kawowa Buhari ziyara a garin Takoko shida Jarumansa.
A lokacinda Dan galadiman sokoto suka fito don su yaki Buhari sai ya zabi Sarkin Jama'are Samboli ya jagoranci Mayakan, saboda shi ya fisu sanin Yankin.

A ranar da zasu yaki Buhari kuma a ranar Buhari ya shirya mamaye Garuruwan da suke kudu da Hadejia, sai aka hadu a Garin Shafowa. Yayin da aka hadu aka gwabza fada Buhari yaci Galaba a kansu duk suka gudu, Sarkin Hadejia Ahmadu yayi kokarin ya Gudu Kasar Kano amma sai Barde Risku ya bishi ya Kashe shi.

Bayan Yakin Takoko yazo karshe kuma an kashe Sarkin Hadejia Ahmadu Amma ba'a son ran Buhari ba kuma aka masa Sallah aka kaishi Hadejia aka binne shi, sannan sai Buhari ya koma Hadejia yaci gaba da Mulki. Sakamakon wannan yakin, dangantaka ta sake baci tsakanin Hadejia da Sokoto, kuma Sarkin Musulmi yaki yarda da ya nada Buhari Sarkin Hadejia. Sai ya nada Tukur Na yayari, kanin Sarki Ahmadu kuma yace ya zauna a Mashama a Kasar Katagum a Matsayin sarkin Hadejia ya Gaji dan'uwansa Ahmadu. Amma Tukur bai yarda ya zama Sarkin Hadejia ba saboda yana tsoron Buhari, sai yaga bazai iya yin haka ba. Kuma saboda Gudun kar Buhari ya kasheshi sai Tukur ya Gudu daga Mashema yayi kaura zuwa Kano Lokacin Sarkin Kano Usman Na1(1846-1855) Sai aka Turashi ya Mulki Yayari a Kasar Birnin Kudu. (Yayarin Tukur) Tukur ya zauna acan Har zuwa lokacinda ya Mutu 1909. Buhari kuma yaci gaba da mulkin Hadejia yana kai hare hare a matsayin Jihadi Har saida yakai Gabasawa,Sankara,Ringim da Kuka kwance A Arewa maso yamma. A Kudu saida ya mamaye Kununu,Takalafiya, Kafin baka, Doma, Ruba, Itas da Kwanda. A Gabas kuwa saida ya Mamaye Babuwari, Kazura, Dawah, Gatare da Margadu. Saida Sarki Buhari ya fadada kasar Hadejia tafi Ko ina fadin Kasa a karni na19.