content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Friday, February 19, 2016

TARIHIN HADEJIA.



Takaitaccen Tarihin masarautar Hadejia.


Masarautar Hadejia dadaddiyar Masarauta ce wadda ta kafu shekaru aru aru da suka gabata, daga lokacin kafuwarta kawo yanzu masarautar tayi fice da yin suna bisa ga muhimman tarihi da take dashi. Masarautar Hadejia tana daga cikin masarautu da sarakunan HABE suka mulka kafin Jihadin Shehu Usmanu Danfodiyo, kuma tana daga cikin masarautun da ake kira Hausa Bakwai. Masarautar tana daga cikin Masarautu da suke karkashin Daular Usmaniyya, daga Gabas tayi iyaka da Tsohuwar Daular Borno daga yamma tayi iyaka da Masarautar Kano, daga Kudu kuma tayi iyaka da Masarautar Katagum sannan daga Arewa tayi iyaka da Masarautar Gumel. Birnin masarautar yana cikin garin Hadejia dake Arewa maso gabashin Jigawa a Arewacin Nigeria, sunan garin ya samo asali ne daga wani Maharbi wadda shine ya kafa garin wato HADE, da kuma Matarsa JIA. Sunayen wadannan mutane shi aka hada ya zama HADEJIA, domin a lokacin mutanen wasu garuruwa in zasu zo sukan ce mun tafi garin Haden jiya, wato ana masa Lakabi da sunan Matarsa. Saboda takaita kalma ta Hausawa shine yasa aka hade sunan ya zama Hadejia. 

Masarautar Hadejia tana da fadin kasa wadda ta kai Murabba’in kilo mita dubu shida da dari tara da sittin da uku(6963), wannan yanki yana da shimfidaddiyar kasa mai kyau wadda ake kwatanta yanayinta da na kasar Chadi, kuma tana da Jigayi masu tarin yashi da kuma kwari mai tabo da laka amma bada da tsaunuka ko Duwatsu. Kasar Hadejia tana da Kogi wadda ya kasance akwai ruwa kowane lokaci, sannan tana da fadamu masu yawa wadanda suke kafewa lokaci zuwa lokaci.

Kogin kasar Hadejia ya taso ne daga Kudancin Katsina ta Arewa da Zaria sannan ya nufi Arewa maso gabas ya shigo ta Kasar Kano ya ratsa kasar Hadejia, sannan ya nufi Tafkin Chadi. Wannan Kogi ya ratsa ne ta Kudancin Hadejia da Gabashinta, wannan bangare ne da yake samarda ruwan sha da kamun kifi da kuma aiwatar da Noman rani. A lokacin damina kogin yakan cika inda yake samarda kananan fadamu a sassa daban daban wadda ake amfani dasu a wajen noman lambu. A bangaren Noma Masarautar Hadejia tana gabatarda noma a lokuta biyu wato Rani da Damina, inda masana yanayin kasa suka tabbatar cewa duk abinda aka shuka a wannan kasar zai fito yayi kyau saboda yanayin kyawun kasar. 

A bangaren kasuwanci kasar Hadejia ta shahara wajen saye da sayarwa tun kafin Jihadi, domin ta zama wata mahadar kasuwanci ce tsakanin Daular sokoto da Daular Borno. Mutanen Masarautar suna da sana’oinsu da dama kama daga sana’ar hannu zuwa Fatauchi da sauransu. Kasar Hadejia tana da kasuwanni da yawa wadanda suke ci a dukkanin sati sannan da masu ci a kowacce rana.

Masarautar Hadejia tana da Kabilu da yawa wadanda suke yarensu da Al’adunsu sun banbanta kuma suna zaune a yankuna daban daban na kasar, Kabilun kuwa sun kunshi Hausawa, Fulani, mangawa, Ngizmawa, koyamawa, Baddawa, da sauransu. Wadannan Kabilu kowanne da irin yarensa da kuma Al’adarsa da irin tsarin zamantakewarsu, sai dai duka suna bin Tafarkin Addinin Musulunci ne tun bayan Jihadin Shehu Usman Danfodiyo.

posted from Bloggeroid

Tuesday, October 6, 2015

KO KUN SAN?........

KO KUN SAN?.....
A shekarar 1971 anyi wata gagarumar yunwa da fari wanda aka sawa suna KWAKWUDUBA, a wannan lokacin hatta fadamu da koguna duk sun kafe babu ruwa, kuma abinci yayi karanci ga mutane. Hakan tasa mutanenmu musamman wadanda garuruwansu yake kusa da Kogi (Masunta) sukayi Kaura daga garuruwansu suka nufi Gabas. Wasu sun wuce har Chadi wasu kuma suka shiga har Kamaru, yayinda wasunsu suka tsaya a garin Baga.

Koda yake a lokacin wannsn garin da ake Kira Doran Baga mutanenmu ne suka je suka kafa Daba a kusa da gabar Kogi. Anan ne sukaci gaba da zamansu suna Kamun Kifi da sauran Albarkatun ruwa sannan su sarrafa su kawo Maiduguri da wasu sassa na jihar Yobe su sayar. Haka gari yaci gaba da girma sakamakon zuwan mutane Masunta domin su samu abinda zasuci da Iyalensu. Sakamakon gari ya zama gari har sai ake kiran Dabar tasu DORON BAGA.

Akasarin mutanen da suka tafi daga kasar Hadejia mutanen Kafinhausa ne da kuma yankunan Kirikasamma da Guri, idan ka lissafa wancan lokacin zuwa yau zai baka shekara 44. Wadannan mutanen wasunsu sun bar garuruwansu ba tare da suna dawowa suna gaida Iyayensu ba, wasunsu kuma har iyayen nasu suka bar Duniya basuzo sun gansu ba,wasu a cikinsu sun manta yanda yanayin garinsu ma yake saboda sun samu Duniya acan. Da yake ba duk aka taru aka zama daya ba wasu sukan zo su gaida 'yan-uwansu da abokan Arziki sannan su koma tunda Allah yayi zamansu acan.

RIKICIN BOKO HARAM....
A cikin Shekarar 2008/2009 Rikicin Boko Haram ya faru a Gabashin Nigeria, musamman yankunan Jihar Borno da Yobe da wasu sassa na Adamawa da Bauchi da Gombe, wanban rikici yayi Asarar Rayuka da Dukiyoyi masu dinbin yawa, inda akayi ta kone Gidaje da Kasuwanni da wuraren Sana'a. Wannan ne yasa wadancan mutane da na Ambata a sama wadanda Kwakuduba tasa suka bar garuruwansu sai suka fara tunanin su dawo gida, sakamakon fadin Hausawa " Giji Lahira ce" anan ne fa suka fara dawowa ba tare da abinda suka tara a can ba, wasu sun dawo gida sun tarar duk wadanda suka sani sun mutu wasu kuma tsufa ya kama su.