content="3wuzvociws0zc1ytgiyfl4yav6jy8f" /> HADEJIA A YAU!

Ismaila A sabo Hadejia

Ismaila A sabo Hadejia
(1)Wannan dai shine Hotona, wadda Idonku yake kallona. (2) Bayan na tafi gun Sarkina, zaku tuna ni watan wata rana. (3) In wani yayi kiran sunana, sai ku cane Allah yaji kaina. (4) Koda zakuyi jimamina, sai ku yimin addu'ah bayana. Marigayi Aliyu Akilu.

Sunday, February 12, 2017

TARIHIN ƊAN HAUSA (Sir Hanns Vischer)

HADEJIA A YAU!


An haifi Ɗan Hausa a cikin shekarar 1876, bai fara aiki a ko ina ba sai a Nigeria a cikin shekarar 1903. ya fara aiki a matsayin mataimakin Razdan, kuma sunansa shine Sir. Hanns Vischer, ya fara zuwa Ƙasar nan akan aikin Mishan ne. ya fara zuwa ƙasar nan ne tare da Dr. W.R.  Miller da Sarkin Hausa Reb. G.P. Bargery, farkon samun aikinsa an ajiyeshi a waɗansu wurare harma ya taɓa zama a Barno. yana can Barno ne yayi tafiya da Ayarin Raƙuma daga Tarabulus zuwa Barno ta hanyar Marzuk. har ya rubuta littafi akan tafiyarsa, wadda ya sakawa suna ƙetarar Sahara. yayi wannan tafiya tare da wani yaronsa da ake ƙira Sa'id. shi Sa'id ya daɗe yana Masinja sai a shekarar 1945 ya rasu, duk waɗanda sukayi makaranta a Nasarawa ta kano sun sanshi.

Cikin shekarar 1908, Ɗan Hausa ya zama gwamnan makaranta har yaje ƙasar Sudan don ya koyo yadda za'a shirya Al'amarin Ilmi anan. A shekarar 1910 ya kafa makarantar Turawa a Nasarawa dake Kano, yara da samarin da aka buɗe makarantar dasu bayan shekara uku kuma sai su fita suje suyi koyarwa a makarantu na ƙasashensu, kamar su Katsina, Sokoto, Barno, Bidda da Zariya. Wannan makaranta ta Ɗan Hausa tana nan a kusa da ofishin Razdan na Kano kuma har yanzu wannan gida yana nan. Cikin shekarar 1915 ya shiga aikin soja har ya zama laftanal aka gama shi da masu kula da shirin labaran yaƙi, ana nan har ya zama kyaftin har dai ya kai matsayin Manjo. Cikin watan Yuli 1917 Ɗan Hausa ya koma Ingila sakamakon Jinya da ta dameshi, amma dukda haka bayan ya koma Ingila yaci gaba da Taimakon ƙasar nan ta hanyar Ilmi. 
Ɗan Hausa yakan riƙa bada labarin zamansa a ƙasar nan har yakan riƙa bada labarin wani Masinjan Razdan na ƙasar nan Mr. George Tomlinson, lokacin da Masinjan zai je Hajji sai da ya isa Bahar Muhid aka ce ya makara, da zai koma gida ya kewayo ya biyo ta Bahar Rum. har ya isa Birnin Southampton inda Ɗan Hausa yake aiki. anan ya zauna a tashar Jirgin Ruwa tare da sauran fasinja, amma da 'yan Gadin sukaga irin siffarsa sai suka ƙi yarda dashi suka kai shi wurin Ɗan Hausa. Shi da ganin mutumin ya san Bahaushe ne amma Ɗan Hausa bai nuna masa ya iya Hausa ba, sai ya faɗa shi da tambaya da turanci, Bahaushen nan tsoro ya kama shi, amma da yaji Ɗan Hausa ya masa magana da Hausa sai yayi ta kuka don murna. ya sa aka bashi masauƙi mai kyau kuma ya gamashi da Takarda cewa mutumin nan abokin aikinsa ne na Africa. kaga bai taɓa sanin mutumin ba amma saboda yana ƙaunar mutanen  Africa yayi masa wannan Darajar. Cikin 1917 aka kai Ɗan Hausa ofis ɗin wakilin Ingila dake Spain ya zauna acan har aka gama yaƙi.
A shekarar 1923 ya zama sakataren wata jam'iyya mai lura da yadda za'a shirya zancen ilmi a ƙasashen da suke ƙarƙashin mulkin Ingila, kafin ya huta a wannan aiki ne ya samu bubbar lambar Girma ya zama ''Knight'' yana cikin waɗanda suka kafa jam'iyya mai lura da zancen harsuna na Africa watau ''Institute of African Languages and cultures''
Mallam Bello Kagara yace.... 

Haƙiƙa ya cancanci ace dashi Ɗan Hausa, don dabarar sa da yayi nufin bude makarantu anan Nijeriya ta Arewa sai yaje Sakkwato a hankali ya fara da can ya ɗauko ta daga tushe. Bayan haka kuma yaga babu inda ya kamata ya kafa makarantar sai tsakiyar jama'a watau Birnin Kano, sai yaje Nasarawa gabas da kano ya bude ta". Da fari bai ɗauki kowa ba sai 'ya'yan sarakuna, da Hakimai, da Alkalai, da shaihunnan maluma. 

Akwai manyan Sarakuna daga cikin Almajiran sa, kamar sarkin Gwandu da Sarkin Zazzau, da Lamidon Adamawa Mustapha da Sarkin Yawuri, Hakimai kuwa Allah yayi yawa dasu! Sunan Ɗan Hausa har abada bashi ɓata anan ƙasar musamman a ƙasar Kano.  


Malam Bello Kagara yace... "babu abinda yake ban mamaki kamar zamanmu dashi a Nasarawa, ga Almajiran sa cikin Aji da Amawali da Alkyabbu, dasu da malamai sun zama bubba da hula yaro da hula, ga Dawakai da zagage a ƙofar makaranta duk na Almajiran sa ne suna jira a tashi su hau. Amma duk da haka Ɗan Hausa ya ƙyale mu, kowannen mu in safiya tayi zamuyi shara tun daga ciki har waje, ga Barorinmu na kallo basu da ikon su karbe mu. Mu ratsa Kano har Dala mu ɗauko fid da sartse a kai, alhali kuwa ga Dawaki da zagage da Alkyabbu sun riƙe a ƙofar makaranta".
A cikin 1913, yaga malamai sun samu sai ya fara bude makarantu a manyan Alƙaryu don a watsa Ilmi a ko ina, dubi yanzu yadda abu ya tabbata. Amma kam kada ka tona wahalar da Turawan farko suka sha kafin Ilmin Boko ya tabbata..... 

MADOGARA.... 
Gaskiya tafi kobo ta 175.
Sir. Hanns Wikipedia 
Eap.bl.uk. 

Sunday, January 15, 2017

SARKIN MUSULMI SIR. ABUBAKAR III.

HADEJIA A YAU!


SARKIN MUSULMI ABUBAKAR. 
Cikin 1902, ana kamar badi Turawa zasu zo Sokoto anka haifeni a wani gari wai shi Dange. Tun ina dan shekara Bakwai (7) Marigayi Sarkin Musulmi Hassan ya riƙe ni, da na dan yi wayo na isa fara karatu, da yake Sarkin Musulmi Malami ne bai kai ni kowace makaranta ba, sai ya tsareni nan gaba nai shina koya min karatu. Shina kuma kula dani da hana ni yawan Shedana irin ta yara. 

Lokacin da Sarkin Musulmi Hassan ke Mallamin Uban Kasar Dange (Hakimin Dange),  da na fara ido wajen Karatu sai nayi ta taimako nai wajen Aikinga. Muna nan haka cikin Shekarar 1923, Sarkin Musulmi Hassan ya sami Sarautar Sarkin Bauran Dange. Da ya sami wannan Sarautar ni kuma sai ya maishe ni matsayi nai na zama ni am Mallami nai. (Malamin Hakimi). 

Muna nan haka har cikin shekarar 1931, Allah ya nufa Sarkin Musulmi Hassan ya zama Sarkin Musulmi. Da anka natsa sai ya dauko ni daga Dange ya maida ni Sokoto ya nada ni Sardauna, na zama daya daga cikin mataimaka nai ga harkokin kasa.  A cikin Birni kuma ya sa in rinka kula da dukkan wurare na Aiki, kamar su Gidan Yari,  Gidan Ayyuka, likitocin Shanu, Gandun Daji, Dagarawa da dai Sauransu. A wannan lokacin har Kaduna nazo koyon Aikin 'yan Doka dan in samu sanin hanyar taimakonsu. In ko na fita Rangadi in ka jini a wajen wanga Uban kasa yau gobe sai ka jini a wajen wancan, musamman lokacin Haraji ko Jangali. Wani lokaci nakanyi wata biyar ko shida ban leko cikin Birni ba. 

Muna nan haka sai anka yi mani  Uban Kasar Talatar Mafara, nayi watanni hudu (4) ina wagga Sarauta, sai Allah ya yiwa Sarkin Musulmi Hassan rasuwa cikin Shekarar 1938, Allah shi gafarta masa Amin. Bayan rasuwa tai ni kuma Allah ya kawo ni wagga Matsayi. Ina fatan Ubangiji Allah shi taya ni rikawa. 

Sarkin Musulmi Abubakar shine dan Usman,  Usman dan Sarkin Musulmi Mu'azu (wato uban Marigayi Sarkin Musulmi Hassan) Sarkin Musulmi Mu'azu dan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello, Sarkin Musulmi Bello dan Shaihu Usman Dan Hodiyo. Allah shi gafarta musu baki daya Amin. 

Sarkin Musulmi Abubakar bai shiga makarantar Turawa ba amma ya koyi Rubutu da Karatu irin nasu. Sarkin Musulmi Abubakar  shine Sarkin da yafi kowa dadewa a Sarautar Sarkin Musulmi, domin ya shekara Hamsin yana kan Halifar Shehu  Usman Dan Hodiyo. Ya fara Sarauta tun lokacin Turawa,  An nada shi ranar 17/yuni/1938, Razdan na Sokoto  Commander J. Carrow shine ya nada shi. Sarkin Musulmi Abubakar yayi Aiki da Gwamnatoci  Takwas (8), a Nigeria bayan samun 'yancin  Kai.  Bayan zamansa Sarkin Musulmi shine ya Baiwa Ahmadu Bello Sarautarsa ta Sardauna a cikin shekarar 1938. Ya rasu yana da shekaru 85 a Duniya,  ya rasu a cikin shekarar 1988. Allah ya Gafarta masa da rahma tare da Al' ummar Annabi baki daya. 


Madogara....... 
1. Sultan Abubakar lll, Littafin Jean Boyd da Hamzat M. Maishanu.
2. Sultan Muhd. Maccido  in the shadow of his Ancestors,  Littafin Hassana Isma'ila Bichi.
3. Gaskiya ta fi Kobo ta Hudu (4) 1939.